Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiShugabar ma’aikatan gwamnati ta amince da kuskure kan hukumar PFIPC

Shugabar ma’aikatan gwamnati ta amince da kuskure kan hukumar PFIPC

Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Didi Esther Walson-Jack, ta bayyana cewa ofishinta ya amince da gudanar da ayyukan hukumar PFIPC ne bisa wasu takardu da aka gabatar masa, waɗanda daga baya aka gano cewa na jabu ne.

Ta ce takardun sun haɗa da wasiƙar naɗin Adeniyi Adeyemi a matsayin Darakta Janar da kuma abin da aka gabatar a matsayin dokar kafa hukumar.

A cewarta, rashin gudanar da cikakken bincike kafin amincewa da takardun ne ya sa ba a gano cewa ba su da inganci ba.

Sai dai bayan binciken da Majalisar Wakilai ta fara, ofishinta ya gudanar da nasa binciken, wanda ya tabbatar da cewa takardun da aka yi amfani da su na bogi ne.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments