Rundunar haɗin gwiwa ta jihar Kano mai yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da fataucin haramtattun ƙwayoyi ta fara aikin samame na farko ƙarƙashin jagorancin CSP Bashir Gwadabe, Kwamandan sashen anti-daba.
An gudanar da samamen ne da misalin ƙarfe 5:15 na yammacin ranar Alhamis, inda jami’an suka kai aiki a harabar Sakatariyar Audu Bako, Kofar Dan’agundi, Filin Mahaha da kuma tsakiyar birnin Kano.
A cewar bayanin aikin, jami’an sun kama mutane 13 da ake zargi a harabar Sakatariyar Audu Bako. Haka kuma, an ce an gudanar da aikin cikin nasara ba tare da wata turjiya ko ƙorafi daga jama’a ba.
Wata sanarwa da daya daga cikin mambobin kungiyar, Nasiru Salisu Zango ya yada ta kafar Whatsapp ya bayyana cewa daga daga cikin waɗanda aka kama akwai Bala Rabiu (Shala), Aminu Ibrahim (Babba), Idris Isa, Danladi Musa, Umar Salisu (Bahago), Sulaiman Adamu (Yaya), Anas Ahmad (Cow Boyi), Najib Muhammad (Hiji), Salisu Imran, Abubakar Inuwa, Nata’ala Ali (Baban Sokoto), Hamisu Kabiru (Yakasai) da kuma Muhammad Babale (Batte).
Bayanin ya ce Muhammad Babale na cikin matsanancin maye, lamarin da ya sa aka garzaya da shi asibiti domin kula da lafiyarsa.
Hukumomin rundunar sun ce za su ci gaba da irin waɗannan samame a sassa daban-daban na jihar domin daƙile shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sauran ayyukan da suka shafi fataucin haramtattun ƙwayoyi.