Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiYan bindiga sun kai hari kotu a Katsina, alƙali ya tsira da...

Yan bindiga sun kai hari kotu a Katsina, alƙali ya tsira da kyar

Wani alƙalin Kotun Shari’a da ke ƙauyen Gwarjo, ƙaramar hukumar Matazu a Jihar Katsina, ya tsallake rijiya da baya bayan wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari har cikin harabar kotun.

Rahotanni sun bayyana cewa alƙalin ya hango maharan tun kafin su isa kotun, lamarin da ya ba shi damar tserewa ta taga.

Daga nan wani ɗan acaba ya taimaka masa ya bar yankin cikin gaggawa kafin maharan su iso.

An ce maharan sun shiga kotun suna harbe-harbe tare da tambayar inda alƙalin yake.

Bayan sun gano cewa ya tsere, sun yi barazanar kashe shi idan ya sake dawowa gudanar da zaman kotu a yankin.

Lamarin ya sake jefa mazauna yankin cikin fargaba, yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan Jihar Katsina.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments