Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiSama da mutum 170 na hannun masu garkuwa da mutane, ƙungiyoyi sun...

Sama da mutum 170 na hannun masu garkuwa da mutane, ƙungiyoyi sun nemi agajin Gwamnati

Ƙungiyar Kaiama Development Association (KDA) da Batombu Unity Development Initiative (BUDIA) sun buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ƙara ƙaimi wajen ceto sama da mutum 170 da aka sace a harin da aka kai ƙauyen Woro da ke Ƙaramar Hukumar Kaiama a Jihar Kwara a watan Fabrairun 2026.

Ƙungiyar Kaiama Development Association (KDA) da Batombu Unity Development Initiative (BUDIA) sun buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ƙara ƙaimi wajen ceto sama da mutum 170 da aka sace a harin da aka kai ƙauyen Woro da ke Ƙaramar Hukumar Kaiama a Jihar Kwara a watan Fabrairun 2026.

Ƙungiyoyin sun yi wannan kira ne a wani taron manema labarai da suka gudanar a Abuja, inda suka yi gargaɗin cewa matsalar tsaro a yankin Borgu na iya rikidewa zuwa babbar matsalar ta’addanci idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba.

Mai magana da yawun ƙungiyoyin, Farfesa Umaru Semo, ya ce harin da aka kai ƙauyukan Woro da Nuku a ranar 3 ga Fabrairu ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 200, yayin da aka yi garkuwa da fiye da mutum 170, ciki har da mata, masu shayarwa da yara. Ya kuma roƙi gwamnati da ta ceto matan da ’ya’yan Sarkin Yashikira da aka sace a wani hari daban.

Ƙungiyoyin sun kuma buƙaci a ƙara tura jami’an tsaro zuwa ƙananan hukumomin Kaiama da Baruten na Jihar Kwara, da Borgu da Agwara a Jihar Neja, da kuma wasu sassan kudancin Jihar Kebbi domin hana sake aukuwar hare-hare.

A nasa jawabin, Daraktan CARE International a Najeriya, Dakta Hussaini Abdu, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta samar da hanyoyin magance matsalar tsaro na dindindin a yankin Borgu. Ya kuma yi zargin cewa an soke ziyarar da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, zai kai Woro bayan harin domin kauce wa nuna lalacewar hanyar Ilorin zuwa Woro da kuma rashin ci gaban ababen more rayuwa a arewacin Jihar Kwara.

Ƙungiyoyin sun kuma bukaci Gwamnatin Tarayya ta bai wa ceton mutanen Woro da Yashikira irin muhimmancin da aka bai wa wasu hare-haren sace mutane a wasu sassan ƙasar. Sun ce hakan zai taimaka wajen dawo da amincewar al’umma da kuma ƙarfafa matakan tsaro a yankin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments