Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya sanar da Jerry Adams a matsayin abokin takararsa na mataimakin gwamna a zaɓen 2027.
Gwamnan ya bayyana cewa zaɓin Jerry Adams ya samo asali ne daga burin gina gwamnati mai haɗin kai, adalci da bai wa kowa dama ba tare da la’akari da bambance-bambancen addini ko ƙabila ba.
A cewarsa, haɗin tikitin zai ƙara ƙarfafa haɗin kan al’ummar Kaduna tare da ci gaba da aiwatar da manufofin ci gaba da gwamnatin sa ta fara a faɗin jihar.