Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeTinubu ya bukaci likitocin Najeriya da ke kasashen waje su dawo gida

Tinubu ya bukaci likitocin Najeriya da ke kasashen waje su dawo gida

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga likitocin Najeriya da sauran ƙwararrun ma’aikatan lafiya da ke zaune a ƙasashen waje da su dawo gida, tare da ƙarfafa sauran abokan aikinsu su ma su dawo domin ba da gudunmawa wajen bunƙasa fannin lafiya a ƙasar.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar Kungiyar Likitocin Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, ƙarƙashin jagorancin Shugabar NiDCOM, Abike Dabiri-Erewa, a wani ɓangare na bikin Ranar ’Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje ta 2026.

Shugaban ya ce ya taɓa rayuwa da aiki a Amurka kafin ya dawo Najeriya, yana mai bayyana cewa ƙwarewar da ya samu a can ta ƙara masa tabbacin cewa Najeriya ita ce ƙasar da ta fi dacewa da hidima.

Ya kuma jaddada cewa gudunmawar likitocin Najeriya da ke ƙasashen waje na da matuƙar muhimmanci wajen inganta tsarin kiwon lafiya a ƙasar.

A nata ɓangaren, Shugabar NiDCOM, Abike Dabiri-Erewa, ta ce likitocin sun shirya amfani da iliminsu da ƙwarewarsu domin tallafa wa shirin gwamnatin Tinubu na inganta harkokin lafiya a Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments