Saturday, October 17, 2026
HomeLabarai’Yan sanda sun kama wanda ake zargi da yin aikin likita ba...

’Yan sanda sun kama wanda ake zargi da yin aikin likita ba tare da lasisi ba

Wani mutum mai shekaru 39, mai suna Udeme Emmanuel Ekpeme, da aka kama bisa zargin yin aikin likita ba tare da lasisi ba a Jihar Cross River, ya amsa cewa ya yi wa aƙalla marasa lafiya 15 magani tsawon shekaru bayan ya daina karatun likitanci.

Wani mutum mai shekaru 39, mai suna Udeme Emmanuel Ekpeme, da aka kama bisa zargin yin aikin likita ba tare da lasisi ba a Jihar Cross River, ya amsa cewa ya yi wa aƙalla marasa lafiya 15 magani tsawon shekaru bayan ya daina karatun likitanci.

Jami’an ’yan sanda na sashen Uwanse da ke Calabar South ne suka kama shi bayan wata mata mai suna Edemawan Samuel ta kai ƙara tana zarginsa da yin kwaikwayon likita, karɓar kuɗi ta hanyar yaudara da kuma gudanar da asibitin tafi-da-gidanka ba bisa ƙa’ida ba.

’Yan sanda sun ce wanda ake zargin ya karɓi Naira 500,000 daga matar bayan ya yi mata alƙawarin samo wa ’ya’yanta aiki a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Calabar (UCTH).

A cikin bayaninsa, Ekpeme ya ce ya daina karatun likitanci, amma ya sayi kayan aikin gwaji da nufin samun kuɗin da zai ba shi damar komawa makaranta ya kammala karatunsa. Ya ce daga shekarar 2014 zuwa 2026, ya yi wa aƙalla mutane 15 magani duk da cewa ba shi da lasisin yin aikin likita.

Matar da ta kai ƙarar ta ce ta fara zargin Ekpeme ne bayan ya sake neman ƙarin Naira 40,000, yana cewa kuɗin na da alaƙa da harkokin banki wajen samun aikin da ya yi wa ’ya’yanta alƙawari. Ta kuma zarge shi da yi mata da ’ya’yanta allurai a lokacin da yake gabatar da kansa a matsayin ƙwararren likita.

’Yan sandan Jihar Cross River sun tabbatar da kama wanda ake zargin, inda suka ce binciken farko ya nuna cewa ya gabatar da kansa a matsayin likita tare da karɓar Naira 500,000 ta hanyar yaudara. Rundunar ta ce an kwato wasu kayayyakin da ake dangantawa da laifin, yayin da ake ci gaba da tsare shi domin gudanar da bincike, tare da gargadin jama’a da su guji zuwa wajen masu aikin likita marasa lasisi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments