Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiMajalisar wakilai ta amince da kudirin kafa ’yan sandan Jihohi

Majalisar wakilai ta amince da kudirin kafa ’yan sandan Jihohi

Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da kudirin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kafa rundunar ’yan sandan jihohi, bayan kammala karatu a kansa a zaman majalisar da aka gudanar a ranar Alhamis.

Kudirin ya samu goyon bayan ’yan majalisa 311 da suka halarci zaman, lamarin da ya nuna gagarumin goyon baya ga sauyin da ake son yi a tsarin tsaron ƙasar.

Kafin hakan, majalisar ta janye nata kudirin da ta gabatar kan batun kafa ’yan sandan jihohi, sannan ta fara nazarin sabon kudirin da gwamnatin tarayya ta aike mata, inda ta amince da shi bayan kammala karatu a kansa.

Ana sa ran matakin zai zama wani muhimmin ci gaba a ƙoƙarin sake fasalin tsarin tsaro a Najeriya, yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan yadda za a aiwatar da tsarin idan ya kammala dukkan matakan da doka ta tanada.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments