Monday, October 19, 2026
HomeTsaroTinubu ya amince da kafa sabuwar bataliyar sojoji a jihar Kwara

Tinubu ya amince da kafa sabuwar bataliyar sojoji a jihar Kwara

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da kafa sabuwar bataliyar sojoji a jihar Kwara, a wani mataki na ƙarfafa tsaro da kuma ƙara kaimi wajen yaƙi da matsalolin rashin tsaro da sauran laifuffuka a jihar.

Za a girke bataliyar ne a garin Omu Aran, hedikwatar ƙaramar hukumar Irepodun, inda ake sa ran matakin zai ƙara yawan jami’an soji da kayan aikin tsaro da za a tura yankin domin inganta tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da mataimakin babban sakataren yaɗa labaransa, Mashood Agboola, ya fitar a ranar Talata, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A cewar gwamnatin jihar, ana sa ran kafa sabuwar bataliyar za ta taimaka wajen ƙarfafa ayyukan tsaro, dakile ayyukan masu aikata laifuka, da tabbatar da zaman lafiya a Kwara da ma yankunan da ke makwabtaka da ita.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments