Majalisar Wakilan Najeriya ta fara gudanar da cikakken nazari kan kudirin dokar kafa ’yan sandan jihohi, a wani mataki na ci gaba da gyaran Kundin Tsarin Mulkin ƙasar.
Kwamitin Majalisar da ke kula da garambawul ga kundin tsarin mulki ne ke jagorantar nazarin, bayan gwamnatin tarayya ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta gabatar da kudirin domin duba yiwuwar amincewa da tsarin.
Ana sa ran kudirin zai samar da damar kafa rundunonin ’yan sanda a matakin jihohi domin ƙarfafa tsaro, musamman wajen magance matsalolin rashin tsaro da ke addabar sassa daban-daban na ƙasar.
Sai dai batun kafa ’yan sandan jihohi ya dade yana haifar da muhawara, inda wasu ke ganin zai inganta tsaro, yayin da wasu ke nuna fargabar yiwuwar amfani da rundunar wajen cimma muradun siyasa.