Jam’iyyar ADC reshen Jihar Kebbi ta bayyana cewa shari’ar da ake yi wa tsohon Ministan Shari’a kuma tsohon Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami (SAN), ba za ta hana shi ci gaba da shirye-shiryen neman takara a babban zaɓen shekarar 2027 ba.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa bayan taron shugabanninta da aka gudanar a jihar Sokoto, inda ta ce tana kallon shari’ar a matsayin wadda ke da alaƙa da siyasa.
ADC ta jaddada cewa tana da cikakken yaƙinin Malami, tare da bayyana cewa za ta ci gaba da ba shi goyon baya yayin da yake shirin fafatawa a zaɓen 2027.
Jam’iyyar ta kuma ce babban burinta shi ne ƙarfafa tsarinta a Kebbi da sauran sassan ƙasar domin kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a babban zaɓen shekarar 2027.