Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da wasu manyan shirye-shiryen ci gaba guda biyar da darajarsu ta kai Dala biliyan 3.05, da nufin rage talauci, samar da ayyukan yi da kuma inganta rayuwar al’umma a faɗin Najeriya.
Shirye-shiryen sun haɗa da ƙarin tallafin NG-CARES, shirin SOLID na tallafa wa ‘yan gudun hijira da al’ummomin da suka karɓe su, da kuma rukunin shirye-shiryen HOPE da suka shafi inganta shugabanci, harkokin lafiya da ilimi.
A wajen ƙaddamar da shirin a Abuja, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa an tsara shirye-shiryen ne domin mayar da nasarorin da aka samu a fannin tattalin arziki zuwa ci gaban da jama’a za su amfana da shi kai tsaye.
Ministan Kuɗi, Wale Edun, wanda ya wakilci Shugaba Tinubu, ya ce wannan mataki wani bangare ne na ƙoƙarin gwamnati na rage radadin talauci, ƙarfafa tattalin arzikin al’umma da samar da damar dogaro da kai.