Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiRibadu ya gana da sabon jami’in Amurka domin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro

Ribadu ya gana da sabon jami’in Amurka domin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro

Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya gana da sabon Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka mai kula da nahiyar Afrika, Frank Garcia, domin tattauna hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka.

Ganawar ta gudana ne an Abuja yayin ziyarar farko da Garcia ya kai Najeriya tun bayan da aka naɗa shi a wannan muƙami.

Ziyarar na daga cikin rangadin da yake yi a wasu ƙasashen Yammacin Afrika domin bunƙasa alaƙar diflomasiyya da ta tsaro.

Ribadu ya bayyana cewa tattaunawar ta mayar da hankali kan yadda ƙasashen biyu za su ƙara haɗa kai wajen yaƙi da ta’addanci, musayar bayanan sirri, horas da jami’an tsaro da kuma tinkarar sauran barazanar tsaro da ke addabar yankin.

Ya ƙara da cewa bangarorin biyu sun yi nazari kan ci gaban da aka samu a ƙarƙashin shirye-shiryen haɗin gwiwa da ake gudanarwa, tare da sake jaddada aniyar ci gaba da zurfafa dangantakar da ke tsakanin Najeriya da Amurka.

Ziyarar ta zo ne a lokacin da Najeriya ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsaro a wasu sassan ƙasar, lamarin da ya sa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu ke da muhimmanci wajen ƙarfafa yaƙi da ta’addanci da sauran manyan laifuffuka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments