Majalisar Masarautar Sarkin Musulmi ta bukaci daukacin al’ummar Musulmi a fadin Najeriya da su fara neman ganin jinjirin watan Safar na shekarar Hijira ta 1448 AH a yau Talata, 14 ga Yulin 2026, wanda ya yi daidai da ranar 29 ga watan Muharram.
A cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na majalisar, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ya sanya wa hannu, an ce duk wanda ya hangi jinjirin watan ya sanar da hakimi ko mai unguwa mafi kusa domin a isar da rahoton ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar.
Sanarwar ta bayyana cewa Sarkin Musulmi, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ne zai karɓi rahotannin ganin jinjirin watan kafin a sanar da fara watan Safar a hukumance.
Majalisar ta jaddada cewa duban jinjirin wata na daga cikin muhimman al’amuran addinin Musulunci da ake dogaro da su wajen tabbatar da fara sabon watan Hijira.
A ƙarshe, ta yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya ba al’ummar Musulmi ikon sauke wannan ibada yadda ya kamata, tare da karɓar ayyukan ibadarsu.