Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeAU ta yi Allah-wadai da harin RSF kan makarantar ƙananan yara da...

AU ta yi Allah-wadai da harin RSF kan makarantar ƙananan yara da ya kashe mutane 80

Ƙungiyar Tarayyar Afrika ta AU ta yi tir da harin RSF kan wata makarantar ƙananan yara a Kudancin Sudan da ya kashe ɗimbin fararen hula tare da jikkata da dama.

Aƙalla mutane 80 – galibinsu ƙananan yara ne suka mutu a wannan hari na mayaƙan RSF bayan da suka jefa bama-bamai kan wata makarantar ƙananan yara da ke garin Kalogi na yankin Kordafan a kudancin Sudan, daidai lokacin da ake ganin ta’azzarar cin zarafi da kisan babu gaira babu dalili a yaƙin na Sudan da ke tunƙarar shekaru 3 da farowa.

Rahotanni sun bayyana cewa hare-hare 3 RSF ta kai a yankin lokaci guda, inda a farko mayaƙan suka jefa bama-bamai a makarantar ƙananan yara gabanin kai hari wani asibiti kana daga bisani suka sake jefa wani bam kan waɗanda ke ƙoƙarin kai ɗauki makarantar ƙananan yaran.

Shugaban gwamnatin garin na Kalogi da harin ya faru, Essam al-Din al-Sayed ya ce tun a Lahadin da ta gabata ne harin ya faru, amma rashin sadarwa ya sanya gaza samun bayanai har sai a jiya Lahadi.

A cewar al-Sayed yanzu haka babu sadarwa a garin face ta hanyar amfani da Starlink, kuma tsagin RSF da Abdelaziz al-Hilu ke jagoranta ne ke ƙaddamar da hare-haren kan mata da ƙananan yara a yankin.

Tun a watan Afrilu 2023 ne yaƙi ya ɓarke tsakanin Sojin gwamnati da dakarun kai ɗaukin gaggawa na RSF wanda ke matsayin mafi muni da ƙasar ta gani da zuwa yanzu ya raba mutane fiye da miliyan 12 da muhallansu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments