Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga fitattun mawakan Afrobeats da suka haɗa da Davido, Burna Boy da Asake da su kafa gidauniyoyi domin tallafa wa marasa galihu, tana mai cewa gwamnati kaɗai ba za ta iya magance matsalar talauci ba.
Ta bayyana cewa fitattun mawakan da suka samu arziki a harkar nishaɗi na da damar amfani da wani ɓangare na dukiyarsu wajen tallafa wa ƙananan ‘yan kasuwa, matasa da sauran masu ƙaramin ƙarfi domin inganta rayuwarsu.
Oluremi Tinubu ta jaddada cewa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu zai taimaka wajen rage talauci da bunƙasa tattalin arziki, tana mai ƙarfafa attajirai da mashahuran mutane su riƙa mayar wa al’umma da abin da suka samu.
Har ila yau, ta shawarci matasa da kada su raina kowace irin sana’a ta halal.
Ta kawo misalin wani matashi da ya fara sayar da ƙosai bayan ya rasa aikin yi, wanda daga bisani ya faɗaɗa sana’arsa har ya samar wa mutum 12 aikin yi.