Sunday, October 18, 2026
HomeTsaro‘Yan bindiga sun hallaka jami’in tsaro, sun yi garkuwa da mutane uku...

‘Yan bindiga sun hallaka jami’in tsaro, sun yi garkuwa da mutane uku a Abuja

Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai hari a yankin Mpape da ke Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja, inda suka kashe wani jami’in tsaro tare da yin garkuwa da mutum uku, ciki har da wani fasto.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na dare a wani sabon layi da ake kira Yellow House.

Maharan sun yi ƙoƙarin kai hari kan wani gida, amma jami’an ƴan sanda da aka sanar da aukuwar lamarin sun isa wurin cikin gaggawa, lamarin da ya haddasa musayar wuta tsakanin bangarorin biyu.

Bayan sun gaza cimma manufarsu, maharan sun janye daga yankin.

A yayin da suke tserewa, sun yi garkuwa da wani fasto da ke kan hanyarsa ta komawa gida, inda suka fitar da shi daga motarsa.

Haka kuma sun sace wasu mazauna yankin biyu da suka tarar a hanya.

An gano motar faston da aka sace a gefen wata hanya a cikin unguwar bayan jami’an tsaro sun bi sawunta.

Har ila yau, wani mazaunin yankin ya samu rauni bayan maharan sun harbe shi a ƙafa.

An garzaya da shi asibiti domin samun kulawar likitoci.

Rahotanni sun kuma ce an ci gaba da jin karar harbe-harbe a wasu sassan Mpape har zuwa kusan ƙarfe 2:00 na dare.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, kakakin rundunar ƴan sandan Babban Birnin Tarayya (FCT), SP Josephine Adeh, ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments