Sunday, October 18, 2026
HomeSiyasaADC ta zargi APC da neman tsare El-Rufai har bayan zaɓen 2027

ADC ta zargi APC da neman tsare El-Rufai har bayan zaɓen 2027

Jam’iyyar ADC ta zargi jam’iyyar APC da ƙoƙarin ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, har sai bayan babban zaɓen shekarar 2027.

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar ADC, Bola Abdullahi, ya ce APC na tsoron irin tasirin siyasar El-Rufai da kuma ƙarfin da haɗakar jam’iyyun adawa za ta samu idan aka sake shi.

A cewarsa, ci gaba da tsare tsohon gwamnan na da alaƙa da siyasa, yana mai zargin cewa manufar ita ce hana shi taka rawar gani kafin zaɓen 2027.

Sai dai, ya zuwa yanzu, jam’iyyar APC da hukumomin da abin ya shafa ba su fitar da wata sanarwa a hukumance da ke mayar da martani kan wannan zargi ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments