Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiCutar Kwalara ta hallaka mayaƙan ISWAP tara a Borno

Cutar Kwalara ta hallaka mayaƙan ISWAP tara a Borno

Rahotanni sun bayyana cewa wata barkewar cutar amai da gudawa ta yi sanadiyyar mutuwar mayaƙan ƙungiyar ISWAP tara a yankin Timbuktu Triangle na jihar Borno, wanda aka sani a matsayin ɗaya daga cikin manyan maboyar ƙungiyar.

Masanin harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya ce cutar ta bazu a sansanonin ƙungiyar sakamakon ƙarancin tsafta da kuma rashin samun kulawar lafiya.

Bayanan sirri sun nuna cewa wasu mayaƙa biyu da suka kamu da cutar an harbe su ne daga hannun takwarorinsu bayan ƙoƙarin kai su jinya a ƙauyen Kimba ya ci tura.

Rahotannin sun kuma bayyana cewa hare-haren da dakarun Operation Hadin Kai ke ci gaba da kai wa sun lalata hanyoyin da ake bi wajen kai wa ƙungiyar magunguna da sauran kayan jinya, lamarin da ya ƙara ta’azzara matsalar lafiyar mayaƙan.

Majiyoyin tsaro sun buƙaci a ci gaba da kakaba matsin lamba tare da dakile duk wani yunƙurin kai wa ƴan ta’addan magunguna ko kaya jinya, domin ƙara raunana ƙarfin ƙungiyar da rage damar ci gaba da kai hare-hare a yankin Arewa maso Gabas.

A wani ci gaba, rahotanni sun ce wani da ake zargin mayaƙin ISWAP ne, wanda aka horar kan tukin kwale-kwalen yaƙi da amfani da babbar bindigar Dushka, ya miƙa wuya ga dakarun sojojin Najeriya bayan ya tsere daga sansanin ƙungiyar da ke yankin Tafkin Chadi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments