Sunday, October 18, 2026
HomeTsaroGwamnatin tarayya ta kubutar da ɗalibai 100 da aka sace a jihar...

Gwamnatin tarayya ta kubutar da ɗalibai 100 da aka sace a jihar Neja

Majiyoyi sun tabbatar da cewa ɗaliban da aka sace daga St. Mary’s sun samu ‘yanci cikin koshin lafiya

Gwamnatin tarayya ta samu nasarar kubutar da ɗalibai 100 da aka sace daga makarantar St. Mary da ke Papiri, karamar hukumar Agwara a Jihar Neja da aka sace makonni biyu da suka gabata.

Majiyoyin tsaro sun shaida wa TheCable a ranar Lahadi cewa an sako yaran, kuma suna cikin koshin lafiya. Ana sa ran gwamnati za ta fitar da cikakken bayani game da ayyukan ceto a yau Litinin.

’Yan bindigar sun kai farmaki a ranar 21 ga Nuwamba da misalin ƙarfe 2:00 na dare, inda suka iso makarantar a kan babura. Sun tafi da mutane 315—dalibai 303 da malamai 12—a cikin harin da ya ɗauki kusan sa’o’i uku.


Martanin gwamnati bayan sace daliban Neja

A cikin awanni 24 na farko, yara 50 sun samu damar tserewa daga hannun ‘yan ta’addan da suka sace su. Wannan ya bar mutane 265, ciki har da malamai 12, a kafin labarin ceto mutane 100 a yanzu.

An cimma nasarar ceto daliban ne ne bayan sojoji sun kara kaimi wajen kai hari da sintirin sama a jihohin Neja, Kwara da Kebbi, tare da tura mafarauta cikin dazuka.

Shugaba Bola Tinubu ma ya soke wasu tafiye-tafiyen ƙasashen waje domin sa ido kai tsaye kan lamarin, wanda hakan ya sa aka rufe makarantu na wucin gadi a Jihar Neja da wasu cibiyoyin gwamnati a yankunan da ake ganin suna cikin hadari.


Iyaye na jiran labarin ceto yaransu

Daniel Atori, mai magana da yawun Bulus Yohanna, shugaban CAN na Jihar Niger, ya ce makarantar ba ta samu wata sanarwa a hukumance game da sakin yaran ba.

“Da gaske ne zai kasance babban abin farin ciki idan an sako wasu daga cikin yaranmu… amma har yanzu ba mu samu tabbaci ba,” in ji shi.

Har yanzu ɗalibai 153 da malamai 12 suna hannun masu garkuwa da mutane duk da sakin mutum 100 da aka tabbatar.

SourceThe Cable
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments