Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroA haɗa kai a yaƙi matsalar ta'addanci a Arewa – Sarkin Musulmi

A haɗa kai a yaƙi matsalar ta’addanci a Arewa – Sarkin Musulmi

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a Arewacin Najeriya da su hada kai domin yaki da matsalar ‘yan bindiga, ta’addanci da kuma satar mutane.

Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin taron hadin gwiwa da ya gudana a Kaduna, wanda ya hada gwamnonin jihohin Arewa da sarakunan gargajiya domin tattauna hanyoyin inganta tsaro da zaman lafiya a yankin.

Ya jaddada cewa tabbatar da tsaro ba nauyin gwamnati ko hukumomin tsaro kadai ba ne, illa aiki ne da ya rataya a wuyan kowa.

Ya ce hadin gwiwa tsakanin gwamnatoci, hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya da al’umma shi ne mabuɗin shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi yankin.

A yayin taron, an kuma kaddamar da wani kwamitin amintattu da zai jagoranci ayyukan da suka shafi inganta tsaro a jihohin Arewa 19.

Sarkin Musulmin ya yaba da kafa kwamitin, yana mai cewa matakin ya nuna an fara daukar kwararan matakai wajen fuskantar kalubalen tsaro.

Ya kuma tabbatar wa mambobin kwamitin cewa za su samu cikakken goyon baya daga sarakunan gargajiya domin cimma manufofinsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments