Hukumar Kula da Ilimin Almajirai da Yaran da Ba Su Zuwa Makaranta ta Ƙasa ta ware Naira biliyan 8.4 a kasafin kuɗin shekarar 2026 domin ayyukan ginawa da gyaran tituna, duk da cewa hakan ba ya cikin aikin da doka ta ɗora mata.
Bayanan kasafin kuɗin 2026 sun nuna cewa an ware wa hukumar Naira biliyan 22.82, inda Naira biliyan 21.68 suka tafi ayyukan raya ƙasa, yayin da Naira biliyan 1.14 suka kasance na gudanarwa.
Baya ga tituna, hukumar ta kuma ware kuɗi don sayen motocin asibiti (ambulance), kayan aikin lafiya, na’urorin X-ray da kuma girka fitilu masu amfani da hasken rana a jihohin Ogun, Ekiti da Katsina.
Sai dai dokar da ta kafa hukumar a shekarar 2023 ta ba ta alhakin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, haɗa ilimin boko da na allo, horar da malamai, samar da kayan koyo da kuma kula da tsarin ilimin Almajirai, ba gina tituna ko gudanar da ayyukan lafiya ba.
Masana kan kasafin kuɗi da ƙungiyoyin fararen hula sun bayyana wannan mataki a matsayin karkatar da aikin hukumar daga abin da doka ta tanada, suna gargadin cewa hakan na raunana tsarin ɗaukar alhaki, yana kuma karkatar da kuɗaɗen gwamnati daga ainihin manufar kafa hukumar.
Wata majiya daga Ofishin Kasafin Kuɗi ta ce irin waɗannan ayyukan kan shiga kasafin kuɗin hukumomi ne a lokacin da Majalisar Tarayya ke duba kasafin, domin aiwatar da ayyukan mazabu ta hannun hukumomin gwamnati.
Sai dai ƙungiyoyin fararen hula sun buƙaci gwamnatin tarayya da Majalisar Tarayya su sake duba irin waɗannan tanade-tanade, tare da tabbatar da cewa ana ware wa kowace hukuma ayyukan da suka dace da hurumin da doka ta ba ta.