Nuhu Ribadu, mai ba shugaban Najeriya shawara kan tsaro, ya ce ya gana da wakilan kuma zuwan tawagar na cikin abubuwan da suka amince da shi.
“Tawagar ta ƙunshi ‘yan majalissar wakilai Mario Díaz-Balart, Norma Torres, Scott Franklin, Juan Ciscomani, da Riley M. Moore,” a cewar Ribadu cikin wata sanarwa a shafinsa na sada zumunta.
Kazalika, Jakadan Amurka a Najeriya Richard Mills na cikin tawagar.
Ribadu ya ce sun tattauna matakan yaƙi da ta’addanaci, da zaman lafiya a Afrika, da hanyoyin ƙarfafa ƙawancen tsaro tsakanin Najeriya da Amurka.