Sunday, October 18, 2026
HomeSiyasaGanduje ya ƙaryata jita-jitar zai sauya sheka zuwa NDC

Ganduje ya ƙaryata jita-jitar zai sauya sheka zuwa NDC

Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi watsi da rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar NDC, yana mai cewa wannan labari ba gaskiya ba ne.

A wata sanarwa da tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano kuma tsohon Shugaban Ma’aikatansa, Muhammad Garba, ya fitar, Ganduje ya bayyana cewa har yanzu cikakken mamba ne na APC, kuma bai fice daga jam’iyyar ba.

Ya ce fastocin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta da ke nuna kamar ya koma wata jam’iyya an ƙirƙire su ne domin yaudarar jama’a da kuma haddasa ruɗani a tsakanin magoya bayan APC.

Ganduje ya ƙara da cewa ba ya cikin ‘yan siyasar da ke yawan sauya jam’iyya saboda neman wani abu na siyasa, yana mai jaddada cewa ya kasance mai tsayawa kan akidarsa tun daga farkon rayuwarsa ta siyasa.

Ya kuma tabbatar da cewa bai taɓa tunanin barin APC ba, jam’iyyar da ya jagoranta a matsayin Shugaban ƙasa, tare da kira ga jama’a da su yi watsi da duk wata jita-jita da ke cewa ya sauya sheƙa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments