Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKotu ta ba da umarnin a miƙa wa Ahmad Lawan takardun ƙara...

Kotu ta ba da umarnin a miƙa wa Ahmad Lawan takardun ƙara ta wata hanya ta musamman

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin a miƙa takardun ƙara ga tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ta hanyar da kotu ta amince da ita, a shari’ar da ke ƙalubalantar sahihancin takararsa ta Sanatan Yobe ta Arewa.

Mai shigar da ƙarar ya bayyana cewa duk ƙoƙarin isar da takardun ƙarar ga Ahmad Lawan ta hanyar da aka saba bi bai yi nasara ba, lamarin da ya sa ya nemi kotu ta ba da izinin amfani da wata hanya ta daban domin sanar da shi ƙarar.

Alƙalin kotun ya amince da buƙatar, inda ya bayar da umarnin a yi amfani da substituted service, wato hanyar da doka ta tanada idan ba a samu damar isar da takardu kai tsaye ga wanda ake ƙara ba.

Shari’ar na da alaƙa da rikicin tikitin takarar Sanatan Yobe ta Arewa, inda mai ƙarar ke neman kotu ta binciki sahihancin yadda aka gudanar da batun takarar. Ana sa ran kotun za ta ci gaba da sauraron ƙarar bayan an tabbatar da isar da takardun kamar yadda ta umarta.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments