Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Najeriya ta tsaurara sharuddan karin girma ga ma’aikata

Gwamnatin Najeriya ta tsaurara sharuddan karin girma ga ma’aikata

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa ba za a yi wa manyan ma’aikatan gwamnati karin girma ba sai sun gabatar da cikakkun bayanan tantance nagartar aikinsu.

Sabon tsarin, wanda zai fara aiki a shekarar 2026, ya sanya ingantattun bayanan tantance aiki a matsayin sharadi kafin ma’aikaci ya cancanci shiga jarabawar karin girma zuwa mukamin darakta.

A cewar Ofishin Akanta Janar na Tarayya, ma’aikatan da aka tantance tare da tabbatar da sahihancin bayanansu ne kawai za su cancanci shiga jarabawar karin girma, a wani yunkuri na tabbatar da adalci, rikon amana da kuma bai wa masu kwarewa dama.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments