Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiGwamnan Bauchi ya yi kira ga mahaifinsa da ya biya haƙƙin masu...

Gwamnan Bauchi ya yi kira ga mahaifinsa da ya biya haƙƙin masu ritaya

Shamsuddeen Bala Mohammed, ɗan Gwamnan Jihar Bauchi, ya yi kira ga mahaifinsa, Gwamna Bala Mohammed, da ya gaggauta biyan kuɗaɗen garatutin tsofaffin ma’aikatan jihar da suka yi ritaya.

Ya kuma buƙaci gwamnatin jihar ta ƙaddamar da shirye-shiryen da za su ƙara bunƙasa rayuwar matasa tare da rage matsin tattalin arzikin da al’umma ke fuskanta.

Shamsuddeen ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook mai taken “Bridging the Gap: A Call for a Human-Capital Focused Policy”, inda ya jaddada muhimmancin saka hannun jari a rayuwar jama’a da inganta walwalarsu.

A cewarsa, biyan haƙƙin ma’aikatan da suka yi ritaya da samar da damammaki ga matasa na daga cikin matakan da za su taimaka wajen inganta tattalin arziki da ci gaban jihar.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Shamsuddeen ya yi wannan kira ne a matsayin shawara ga gwamnatin jihar domin ƙarfafa manufofin da suka shafi jin daɗin al’umma da ci gaban ɗan Adam

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments