Saturday, October 17, 2026
HomeKasuwanciBankin Jaiz na shirin bayar da rance ba tare da jinginar kadara...

Bankin Jaiz na shirin bayar da rance ba tare da jinginar kadara ba

Bankin Jaiz Plc ya bayyana cewa yana jiran amincewar Babban Bankin Najeriya, CBN kafin ya ƙaddamar da wasu sabbin tsare-tsaren bayar da rance da za su bai wa ƙanana da matsakaitan kasuwanci (SMEs) damar samun kuɗi ba tare da gabatar da jinginar kadara ba.

Babban Daraktan Bankin, Dakta Haruna Musa, ya bayyana hakan bayan taron shekara-shekara na masu hannun jari na bankin karo na 14 da aka gudanar a Abuja.

Ya ce sabon tsarin zai duba kuɗaɗen shiga da fita na mai neman rance (cash flow) maimakon jinginar kadara, domin sauƙaƙa wa ƙananan ’yan kasuwa samun tallafin kuɗi.

Musa ya ce bankin ya kammala tsara wannan tsarin kuma yana jiran amincewar CBN kafin fara aiwatar da shi. Ya ƙara da cewa za a yi amfani da fasahar zamani domin bai wa kwastomomi damar neman da kuma karɓar rance ta wayar hannu ba tare da zuwa reshen banki ba.

Haka kuma, ya bayyana cewa masu hannun jari sun amince bankin ya tara ƙarin jarin Naira biliyan 150 domin faɗaɗa ayyukansa, bayan samun amincewar hukumomin da abin ya shafa.

SourcePunch
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments