Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiMatatar Dangote ya rage farashin fetur da N50

Matatar Dangote ya rage farashin fetur da N50

Dangote ya sake rage farashin fetur, farashin lita ya sauka zuwa N1,125.

Matatar man Dangote ta sanar da sake rage farashin fetur da N50 kan kowace lita, inda ta saukar da farashin da take sayar wa ’yan kasuwa daga N1,175 zuwa N1,125.

A sanarwar da ta fitar ga abokan hulɗarta, kamfanin ya bayyana cewa ya kuma rage farashin fetur da ake samarwa ta tashar ruwa daga N1,495,215 zuwa N1,428,165 kan kowane tan.

Matatar ta ce matakin ya biyo bayan sauƙin tashin hankali da aka samu a Gabas ta Tsakiya, lamarin da ya taimaka wajen saukar farashin makamashi a kasuwannin duniya.

Kamfanin ya ƙara da cewa yana ci gaba da ƙoƙarin samar da fetur cikin sauƙi tare da tabbatar da wadataccen mai a kasuwar Najeriya.

Wannan shi ne karo na biyu cikin ƙasa da mako guda da matatar ke rage farashin fetur, bayan da a baya ta rage shi da N75 kan kowace lita.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments