Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiAna taimakon yan ta’adda daga wasu kasashen – Sheikh Gumi

Ana taimakon yan ta’adda daga wasu kasashen – Sheikh Gumi

Sheik Gumi ya yi zargin cewa wasu ƙasashen waje masu ƙarfi na da hannu a ta’addanci a Najeriya.

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya sake tayar da muhawara kan rashin tsaro, inda ya yi zargin cewa wasu ƙasashen waje masu ƙarfi na da hannu a ta’addanci a Najeriya.

Ya yi nuni da cewa matsalar da ta ragu a Abuja,Kaduna da Birnin Gwari ta sake ɓullowa a wasu wurare, abin da ke nuna akwai lauje cikin nadi.

Malamin ya ce kabilanci ya shiga matsalar tsaro, abin ya ce yana bukatar kulawa ta musamman daga gwamnatin tarayyar Najeriya

Gumi ya ce kafin wannan sabon tashin hankalin, alamu sun nuna cewa tsaro na inganta musamman a babban titin Abuja zuwa Kaduna.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments