Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKotu ta yanke wa mata hukuncin daurin shekaru biyu kan safarar jariri

Kotu ta yanke wa mata hukuncin daurin shekaru biyu kan safarar jariri

Kotu Ta Daure Mata Shekara 2 Kan Safarar Jariri da Sayar da Shi Kan N200,000

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kalaba, Jihar Cros River, ta yanke wa wata mata mai suna Mbika Asuquo Edem hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan gyaran hali bayan samunta da laifin safarar yara da kuma sayar da wani jariri.

Kotun ta kuma ba ta damar biyan tara maimakon zaman gidan gyaran hali, kamar yadda hukuncin ya tanada.

Hukumar Yaƙi da Fataucin Bil’adama ta Ƙasa (NAPTIP) ce ta gurfanar da wacce aka yanke wa hukuncin bisa zargin safarar yara.

Mai shari’a Rosemary Dugbo Oghoghorie, yayin yanke hukuncin, ta bayyana cewa an tabbatar da laifin da ake tuhumar Mbika Asuquo Edem da shi bisa hujjojin da aka gabatar a gaban kotu.

Kotun ta tabbatar da cewa matar ta aikata laifin safarar yara tare da sayar da wani jariri kan kuɗi Naira 200,000.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments