Cibiyar Kula da Cututtuka da Rigakafi ta Najeriya, NCDC ta bayyana cewa mutane 214 sun mutu sakamakon cutar zazzabin Lassa a Najeriya tun daga farkon shekarar 2026, yayin da adadin masu mutuwa daga cutar ya ƙaru zuwa kashi 25 cikin 100.
A cewar rahoton mako na 23 na NCDC, wannan adadi ya fi na makamancin wannan lokaci a shekarar 2025, inda yawan mace-mace ya kasance kashi 18.9 cikin 100. Haka kuma, an samu ƙarin waɗanda ake zargi da kamuwa da cutar da kuma waɗanda aka tabbatar suna ɗauke da ita.
Rahoton ya nuna cewa an samu sabbin masu kamuwa da cutar a jihohin Ondo, Bauchi, Edo da Ebonyi, yayin da cutar ta bazu zuwa jihohi 23 da ƙananan hukumomi 109 a faɗin ƙasar tun farkon shekarar nan.
NCDC ta ce jihohin Ondo, Bauchi, Taraba, Edo da Benue ne suka fi yawan masu kamuwa da cutar, inda suke da kashi 84 cikin 100 na dukkan rahoton da aka tabbatar. Ta kuma bayyana cewa matasa masu shekaru tsakanin 21 zuwa 30 ne suka fi kamuwa da cutar.
Hukumar ta ce tana ci gaba da haɗa kai da gwamnatocin jihohi da sauran abokan hulɗa domin dakile yaɗuwar cutar, tare da ƙarfafa sa ido, gano masu cutar da kuma kula da marasa lafiya a jihohin da abin ya shafa.