Wata ƙungiyar kare haƙƙin jama’a, (CFRPA) ta aike da wasiƙa ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), tana neman ƙarin haske kan takardun shaidar karatun da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar yayin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023.
A cikin wasiƙar mai ɗauke da kwanan watan 19 ga Yuni, 2026, ƙungiyar ta buƙaci shugaban INEC da ya yi bayani kan batutuwan shari’a da ka iya tasowa dangane da bayanan karatun shugaban ƙasar, da kuma yiwuwar tasirinsu a babban zaɓen shekarar 2027.
Wasiƙar, wadda shugaban sashen shari’a na ƙungiyar, Kalu Agu, ya sanya wa hannu, an karɓe ta a hedikwatar INEC da ke Abuja a ranar da aka aika da ita.
CFRPA ta ce manufar wannan buƙata ita ce ƙarfafa gaskiya da amincewar jama’a ga tsarin zaɓe kafin babban zaɓen 2027.
Sai dai har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, INEC ba ta fitar da wata sanarwa ko martani kan wasiƙar ba, kuma babu wata hukuncin kotu da ya sauya matsayin shari’o’in da suka shafi cancantar Shugaba Tinubu.