Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin kotun tarayya da ta hana jami’an binciken lafiyar motoci ta VIO tsayawa ko ƙwace motoci a hanya ko kuma ƙaƙaba tara ga direbobi.
Kotun, wacce ta ƙunshi alkalai guda uku, ta ce babu wani dalili da zai sa a rushe hukuncin Kotun Tarayya na ranar 16 ga Oktoba, 2024 da ya haramta wa jami’an VIO ƙwace motocin direbobi ƙwace motoci ko musu barazana.
Saboda haka kotun ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar da VIO ta shigar, tana mai cewa ba ta da wani ingantaccen hujja.
A baya, mai Shari’a Nkeonye Maha ta kotun tarayya ta bayyana cewa babu wata doka da ta bai wa VIO ikon tsayawa da kwace ko ƙaƙaba tara ga direbobi saboda wani laifi.
Wannan hukunci ya Sami asali ne daga karar kare hakkin dan adam da lauya Abubakar Marshal ya shigar.
Mai karar ya ce an tare shi da karfi a unguwar Jabi ranar 12 ga Disamba, 2023, kuma aka ƙwace motarsa ba tare da wani dalilin doka ba inda ya buƙaci kotu ta tantance ko abin da jami’an VIO ɗin suka yi ba cin zarafi ba ne ko danniya da kuma saɓawa haƙƙinsa na dan Adam.