Shugaban Amurka, Donald Trump, ya gargadi Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, da ya yi taka-tsantsan wajen tafiyar da rikicin da ke tsakaninsu da Hezbollah a Lebanon.
Trump ya bayyana cewa ci gaba da fadada rikicin na iya kawo cikas ga kokarin samar da yarjejeniyar sulhu tsakanin Amurka da Iran.
Da yake magana da manema labarai yayin taron ƙasashen G7, Trump ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda Isra’ila ke gudanar da yaƙin da take yi da Hezbollah, yana mai cewa ya kamata a kawo ƙarshensa cikin gaggawa.
Ya ce rikicin ya daɗe yana jawo asarar rayuka da lalata dukiyoyi, lamarin da ka iya zama barazana ga shirye-shiryen diflomasiyya da ake yi da Iran.
Trump ya kuma yi zargin cewa hare-haren Isra’ila na haddasa mutuwar fararen hula da rushe gidaje, yana mai cewa ya fi son a nemo wata hanya da za ta rage asarar rayukan marasa laifi.