Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiNYSC ta haramta tura masu yi wa ƙasa hidima zuwa ƙananan hukumomi...

NYSC ta haramta tura masu yi wa ƙasa hidima zuwa ƙananan hukumomi 3 a jihar Kebbi

Hukumar masu yiwa kasa hiding, NYSC ta haramta tura masu yi wa ƙasa hidima zuwa ƙananan hukumomi uku a jihar Kebbi saboda dalilan tsaro.

Hukumar masu yiwa kasa hiding, NYSC ta haramta tura masu yi wa ƙasa hidima zuwa ƙananan hukumomi uku a jihar Kebbi saboda dalilan tsaro.

Hukumar ta bayyana cewa wannan mataki na zuwa ne domin kare lafiyar masu yi wa ƙasa hidima, sakamakon matsalolin rashin tsaro da ake fuskanta a wasu yankunan jihar.

A cewar hukumar, ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Augie, Arewa da Sakaba, inda ba za a ƙara tura sabbin masu hidima ba.

NYSC ta kuma bayyana cewa matsalar rashin tsaro a jihar ta rage yawan masu hidimar da ake turawa Kebbi, har ma ta haifar da ƙarancin likitoci da malamai a wasu wurare saboda rashin masu hidima.

Hukumar ta ce tana ci gaba da tattaunawa da hukumomi domin samun mafita, tare da tabbatar da cewa dukkan masu yi wa ƙasa hidima suna cikin aminci da kariya yayin da suke aikin su.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments