Ƙungiyar da ke fafutukar ci gaban Zamfara ZSCC ta bayyana shirin maka tsohon gwamnan jihar kuma karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, a kotu kan zargin sahihancin wasu takardun karatu da ake alakantawa da shi wajen samun mukaman gwamnati.
A cewar shugaban Kungiyar, Barista Musa Abdullahi, sun kammala tuntubar lauyoyi kuma suna shirin ɗaukar matakin shari’a domin kotu ta binciki gaskiyar takardun da ake magana a kansu.
Ƙungiyoyin sun yi zargin cewa ana amfani da takardar makarantar koyon sana’a ta VTC da ke Bunza wajen shiga siyasa da kuma samun mukamai a gwamnati.
Sun ce akwai tambayoyi kan ko takardun sun cika ka’idojin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya shimfiɗa, inda suka jaddada cewa mukaman gwamnati na buƙatar gaskiya, rikon amana da bin doka.
Haka kuma, sun ce dokokin ƙasa sun haramta jabun takardu ko bayar da bayanan ƙarya domin cin moriyar mukami.
Ƙungiyoyin sun bayyana cewa idan kotu ta tabbatar da zargin, hakan na iya jawo sauke mutum daga mukami tare da yiwuwar gurfanar da shi a gaban doka, har ma da dawo da duk wani alawus ko fa’ida da aka samu ba bisa ƙa’ida ba.