Sunday, October 18, 2026
HomeTsaroGwamnatin Kebbi ta dauki matakan gaggawa kan tsaro

Gwamnatin Kebbi ta dauki matakan gaggawa kan tsaro

Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin sake nazari tare da inganta dabarun tsaro a fadin jihar sakamakon karuwar hare-haren ’yan bindiga a wasu yankuna, musamman kananan hukumomin Wasagu da Argungu.

Umarnin ya biyo bayan wani taron gaggawa da ya jagoranta a Birnin Kebbi, inda jami’an tsaro da manyan jami’an gwamnati suka tattauna hanyoyin da za su taimaka wajen dakile matsalar tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da hada kai da hukumomin tsaro da shugabannin al’umma domin magance matsalar, tare da gabatar da rahoton halin da ake ciki ga Shugaba Bola Tinubu domin neman mafita mai dorewa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments