A wani saƙon bidiyo da ofishinsa ya wallafa, Netanyahu ya bayyana cewa Isra’ila za ta ci gaba da ɗaukar matakan hana Iran mallakar makaman nukiliya ko zama barazana ga tsaron ƙasar.
Ya kuma yi zargin cewa dole ne a hana Tehran sake komawa amfani da barazanar makaman nukiliya da makamai masu linzami da masu dogon zango.
Netanyahu ya yi waɗannan kalamai ne yayin da yake ba sabon shugaban hukumar leƙen asirin ƙasar, Mossad, Roman, umarnin ci gaba da aiwatar da dabarun tsaron Isra’ila da suka shafi Iran.