Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace ƙanwar tsohon Ministan Wutar Lantarki na Najeriya kuma jigo a jam’iyyar APC, Adebayo Adelabu, tare da tagwayen ’ya’yanta biyu a birnin Ibadan na Jihar Oyo.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya auku ne da safiyar Laraba a yankin Challenge, inda maharan masu ɗauke da makamai suka tare motarsu yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa makaranta.
An bayyana sunan matar da aka sace da Olaide Busayo Adegoke John-Paul, mai shekaru 43, yayin da tagwayen ’ya’yanta Peter da Paul masu shekaru 12 suka kasance tare da ita lokacin da aka yi garkuwar.
Mai magana da yawun Adelabu, Femi Awogboro, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da su ne da misalin ƙarfe 7:30 na safe.