Saturday, October 17, 2026
HomeLafiyaNajeriya na shirin killace matafiya don hana yaduwar cutar Ebola

Najeriya na shirin killace matafiya don hana yaduwar cutar Ebola

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da fara killace wasu matafiya da ke shigowa ƙasar daga yankunan da ake fama da barkewar cutar Ebola, a wani yunƙuri na dakile yiwuwar shigowar cutar cikin ƙasar.

Ma’aikatar Lafiya ta bayyana cewa za a gudanar da cikakken binciken lafiya ga matafiya daga ƙasashen Gabashi da Tsakiyar Afirka, tare da ware duk wanda aka gano yana nuna alamun cutar.

Duk da cewa har yanzu ba a tabbatar da samun wani mai ɗauke da Ebola a Najeriya ba, gwamnati ta ce ta ɗauki wannan mataki ne domin kariya da kuma kauce wa wata annoba.

Sanarwar da daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar, Ado Bako, ya sanya wa hannu ta ce za a killace matafiyan da suka nuna alamun zazzaɓi mai tsanani, mura ko wasu alamun farko na Ebola.

Haka kuma, an ƙarfafa sa ido a filayen jiragen sama da hanyoyi ta hanyar amfani da na’urorin gano masu yunƙurin kauce wa binciken lafiya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments