Akalla mutane 17 ne suka rasa rayukansu, ciki har da baƙi masu yawon Sallah guda bakwai, sakamakon wani mummunan hari da ’yan bindiga suka kai a ƙauyen Dangulbi da ke Ƙaramar Hukumar Tureta a Jihar Sokoto.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kai harin ne a ranar Lahadi, 31 ga watan Mayun 2026, inda suka farmaki al’ummar ƙauyen tare da kashe mutane da dama tare da haddasa barna mai yawa.
Mazauna yankin sun shaida cewa ‘yan bindigan, waɗanda suka zo ɗauke da manyan makamai kuma a kan babura kusan 150, sun buɗe wa jama’a wuta ba tare da wata-wata ba.
Haka kuma sun yi awon gaba da kayayyaki daga shaguna, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankin da dama tserewa zuwa dazukan da ke kusa domin tsira da rayukansu.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro ya bayyana cewa maharan sun fito ne daga yankin Bagega da ke Ƙaramar Hukumar Anka ta Jihar Zamfara.
Ya ce bayan sun taso daga Bagega, maharan sun bi ta yankin Barayar Zaki da ke Ƙaramar Hukumar Bukkuyum kafin su isa ƙauyen Gizazza, inda rahotanni suka nuna sun kwana kafin daga bisani su kai harin a Dangulbi.
Harin ya jefa al’ummar yankin cikin firgici da jimami, yayin da mazauna ke kira ga hukumomin tsaro da su ƙara ɗaukar matakan da za su kawo ƙarshen hare-haren ’yan bindiga da suka addabi yankunan Sokoto da maƙwabtan jihohi.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da cikakken bayani kan harin ba.