An wayar da kan ‘yan makaranta mata a Babban Birnin Tarayya Abuja kan yadda za su kula da tsaftar al’ada yadda ya kamata, a wani yunkuri na kawar da kyamar al’ada tare da inganta lafiya da mutuncin yara mata.
Cibiyar Kula da Lafiyar Makarantu da Ilimin Tsaftar Muhalli ce ta shirya wannan shiri yayin bikin Ranar Tsaftar Al’ada ta Duniya ta shekarar 2026 a makarantar Government Girls Secondary School da ke Dutse, Abuja.
Da take jawabi a wajen taron, Daraktar cibiyar, Dokta Folasade Olusola Momoh, ta ce cibiyar na ci gaba da jajircewa wajen inganta lafiya da walwalar matasa, musamman yara mata, ta hanyar shirye-shiryen ilimin lafiya da tallafi a makarantu da al’umma.
Da take magana kan taken bikin na bana mai taken “Mu haɗa kai domin duniya mai sauƙin kula da al’ada,” Momoh ta ce manufar gangamin ita ce kawo ƙarshen kyamar al’ada tare da samar da muhalli mai aminci inda yara mata za su kula da al’adarsu cikin mutunci da kwarin gwiwa.
Ta jaddada cewa bai kamata al’ada ta zama cikas ga karatun yara mata ba, tana mai cewa samun ilimin tsaftar al’ada da kayan amfani na tsafta na taka muhimmiyar rawa wajen inganta zuwa makaranta da kuma nasarar karatu.
Momoh ta yi kira ga gwamnatoci, kamfanoni masu zaman kansu, ƙungiyoyin addini da kuma daidaikun mutane da su tallafa wajen samar da kayan tsaftar al’ada cikin sauƙin farashi da wadatarwa ga yara mata.
Ta ƙara da cewa samar da al’umma mai fahimta da karɓar al’ada na buƙatar buɗaɗɗiyar tattaunawa kan al’ada tare da ƙarfafa tsarin tallafi a gidaje, makarantu da al’umma baki ɗaya.
Shi ma da yake jawabi a wajen taron, Mataimakin Darakta na Sashen Ilimin Lafiyar Makarantu na Hukumar Ilimi ta Babban Birnin Tarayya, Mista Solomon Johnson, ya yabawa cibiyar bisa ci gaba da ƙoƙarin da take yi wajen inganta lafiyar matasa da ilimantar da yara mata kan tsaftar al’ada a yankin.
Johnson, wanda ya wakilci Sakataren Hukumar Ilimi, Dokta Danlami Hayyo, ya bayyana cibiyar a matsayin amintacciyar abokiyar hulɗa wacce shirye-shiryenta suka taimaka wajen ƙarfafa tsarin kula da lafiyar makarantu da inganta walwalar yara mata.
Ita ma jami’ar ilimi ta Hukumar Makarantun Sakandare, Zainab Nuhu, ta bayyana tsaftar al’ada a matsayin wani muhimmin bangare na lafiya, ilimi da ci gaban mutum.
Ta ce yara mata da ke samun ingantaccen bayani da kayan tsaftar al’ada na da damar ci gaba da zuwa makaranta, samun kwarin gwiwa da kuma yin fice a karatu.