Saturday, October 17, 2026
HomeIlimiHukumar JAMB ta cire sharadin UTME ga masu neman fannin ilimin, wato...

Hukumar JAMB ta cire sharadin UTME ga masu neman fannin ilimin, wato Education da noma a kwalejojin ilimi

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Najeriya, JAMB, ta sanar da cewa daga yanzu masu neman shiga shirye-shiryen karatun fannin ilimi, Education da kuma kwasa-kwasan noma da ba na injiniyanci ba a Kwalejojin Ilimi da Kwalejojin Fasaha ba za su sake rubuta jarabawar UTME ba.

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Najeriya, JAMB, ta sanar da cewa daga yanzu masu neman shiga shirye-shiryen karatun fannin ilimi, Education da kuma kwasa-kwasan noma da ba na injiniyanci ba a Kwalejojin Ilimi da Kwalejojin Fasaha ba za su sake rubuta jarabawar UTME ba.

An bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin taron tsara manufofin shiga jami’o’i da sauran manyan makarantu na shekarar 2026 da aka gudanar a Abuja.

A cikin sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce:
“Masu neman shiga shirye-shiryen karatun ilimi da kwasa-kwasan noma da ba na injiniya ba yanzu an cire musu sharadin rubuta UTME.”

Ministan Ilimi na Najeriya, Tunji Alausa, ya bayyana cewa ɗaliban da ke neman shiga shirin NCE ba za a tilasta musu rubuta UTME ba muddin suna da ƙarancin makin da ake buƙata.

Ya ce:
“Masu neman shiga shirin NCE da suke da aƙalla darussa huɗu na credit ba za su sake zama jarabawar UTME ba.”

Sai dai ministan ya jaddada cewa hakan ba yana nufin ba sai sun yi rajista da JAMB ba kafin a ba su gurbin karatu.

“Dole ne irin waɗannan ɗalibai su yi rajista da JAMB, sannan a tantance takardunsu tare da tabbatar da ingancinsu kafin a ba su takardar shiga makaranta ta hanyar CAPS bisa dokokin da ake da su,” in ji shi.

Ministan ya ƙara da cewa sabon tsarin zai kuma shafi masu neman shiga shirye-shiryen National Diploma, ND a fannin noma da sauran darussan da suka shafi noma amma ba na fasaha da injiniya ba.

A cewarsa, an samar da wannan tsari ne domin faɗaɗa damar samun ilimi a manyan makarantu tare da kare ingancin tsarin bayar da guraben karatu.

Ya ce:
“Wannan tsarin zai rage matsin lambar da ke tattare da UTME, sannan ya ƙarfafa mutane su shiga karatun koyarwa da noma, waɗanda suke da matuƙar muhimmanci ga ci gaban ƙasa.”

Wannan mataki na nuni da babban sauyi a tsarin shiga manyan makarantu a Najeriya, inda a baya UTME ke zama babbar hanyar cancantar shiga jami’o’i, kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi.

Ana gudanar da taron manufofin JAMB duk shekara ne domin tsara hanyoyin bayar da guraben karatu, makin da ake yankewa da sauran ƙa’idojin shiga makarantu na sabuwar shekarar karatu.

Ana sa ran sabon tsarin zai samar da wata hanya ta daban ga masu neman karatun ilimi da noma, inda za a fi mayar da hankali kan tantance takardu da gwajin makarantu maimakon UTME.

A baya dai kwasa-kwasan ilimi da noma ba su cika samun gasa mai tsauri ba idan aka kwatanta da kwasa-kwasan da suka fi fice kamar Likitanci, Shari’a da Injiniya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments