Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya kafa Hukumar tattarawa gami raba Zakkah da Wakafi ta jihar, tare da naɗa Farfesa Bukar Muhammad Usman a matsayin shugaban zartarwa na farko na hukumar.
An bayyana cewa an kafa hukumar ne domin kula da tattarawa, gudanarwa da kuma rabon zakkah da wakafi cikin adalci a faɗin jihar, bayan Majalisar Dokokin jihar Borno ta amince da dokar kafa ta a shekarar 2025.
Farfesa Bukar ƙwararren malami ne a fannin adabin Larabci da ilimin addinin Musulunci, kuma yana koyarwa a jamiar jihar Yobe. Ya taba zama shugaban sashen Larabci na jami’ar kafin wannan naɗi.
Haka kuma, Gwamna Zulum ya naɗa Malam Muhammad Ibrahim Muhammad a matsayin memba na Hukumar Kula da Makarantun Sakandire ta jihar domin wakiltar Kudancin Borno, bayan rasuwar Alhaji Ibrahim Sarki.
Gwamnan ya buƙaci waɗanda aka naɗa su yi aiki da gaskiya da ƙwarewa domin inganta ayyukan hukumomin da aka ba su jagoranci.