Wani babban minista a gwamnatin tarayya ya musanta zargin cewa Najeriya na dab da komawa tsarin jam’iyya ɗaya, yana mai jaddada cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da bin ƙa’idojin dimokuraɗiyya.
Da yake magana a wata hira ta musamman da TRT Afrika Hausa, Ministan Yaɗa Labaran Ƙasar, Mohammed Idris ya ƙaryata zarge-zargen da ‘yan adawa ke yi cewa jam’iyyar mai mulki ta APC na ƙoƙarin mamaye fagen siyasa.
Ya bayyana zarge-zargen a matsayin marasa tushe, yana mai cewa Shugaba Tinubu mutum ne da ya shafe rayuwarsa gaba ɗaya cikin harkar dimokuraɗiyya, kuma ba shi da niyyar tauye tsarin jam’iyyu da dama.
A cewarsa, yawan sauya sheƙa da gwamnonin jihohi da ‘yan majalisa ke yi zuwa APC bai kamata a ɗauke shi a matsayin wata manufa ta ƙarfafa jam’iyya ɗaya ba.
Ya ce sauyin jam’iyya abu ne na al’ada a tsarin dimokuraɗiyya, inda ‘yan siyasa ke komawa inda suke ganin manufofi da akidu sun fi dacewa da su.
Ministan ya kuma musanta zargin cewa gwamnati na da hannu a rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyun adawa, musamman jam’iyyar ADC, wadda ke fuskantar wasu sabani a ciki.
Ya ce waɗannan matsaloli al’amura ne na cikin gida da ya kamata jam’iyyar ta warware da kanta.