Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnonin jam’iyyar APC a fadar shugaban kasa da ke Abuja, yayin da shawarwari ke kara karfi gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar.
Taron ya zo ne kasa da sa’o’i 24 bayan shugaban ya yi wani taron gaggawa da shugabannin Majalisar Dattawan Najeriya, a daidai lokacin da ake kara nuna damuwa kan zaben ‘yan takara a jihohi da dama.
Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da
Babagana Zulum na Borno da Hope Uzodimma na Imo da Inuwa Yahaya na Gombe da Hyacinth Alia na Benue, Biodun Oyebanji na Ekiti, da Peter Mbah na Enugu da AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara, yayin da wasu suka samu wakilcin mataimakansu.
A wajen taron gwamnonin, an mai da hankali kan tabbatar da cewa an gudanar da zaben fidda gwani cikin sauki tare da hada kan kowa da kowa.