Ƙungiyar Arewa Consultative Forum, ACF ta bayyana cewa matsalar rashin tsaro a Najeriya ta kai wani mataki mai tsanani, inda ta ce ƙasar na cikin yanayin yaƙi kai tsaye, tare da kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakan gaggawa domin magance wannan matsala.
Wannan matsaya ta fito ne bayan wani muhimmin taro da ƙungiyar ta gudanar a Abuja, inda manyan shugabanni daga yankin Arewa suka halarta domin duba halin da ƙasar ke ciki.
ACF ta jaddada cewa matsalar tsaro ta wuce abin da za a ɗauka a matsayin ƙalubale na yau da kullum, domin ta haɗa da ta’addanci a Arewa maso Gabas, fashin daji da garkuwa da mutane a Arewa maso Yamma da Tsakiya, da kuma rikice-rikicen ƙabilu da na manoma da makiyaya. A cewar ƙungiyar, duk waɗannan matsaloli sun haɗu sun zama babban rikici da ke barazana ga zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.
Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa wannan matsala ta haifar da asarar rayuka da dama, inda dubban mutane suka mutu ko suka rasa matsugunansu a jihohi daban-daban.
Haka kuma, ta nuna cewa iyalai da al’ummomi sun lalace, yayin da jami’an tsaro su ma ke cikin waɗanda ke rasa rayukansu a kokarin kare ƙasa.
ACF ta nuna cewa rashin tsaro yana da mummunan tasiri ga tattalin arzikin ƙasa, musamman a bangaren noma a Arewa. Wannan ya haifar da raguwar samar da abinci da kuma hauhawar farashi, wanda ke ƙara tsananta wahalhalun rayuwa ga ’yan ƙasa.
ƙungiyar ta bukaci gwamnati da ta ɗauki wannan lamari a matsayin abu na gaggawa a ƙasa, tare da karkatar da dukkan albarkatun ƙasa da ƙoƙari wajen dawo da tsaro.
Ta kuma yi gargadi cewa idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, matsalar na iya ƙara tsananta tare da jefa makomar Najeriya cikin haɗari.