Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAn samu karuwar hauhawar farashi a Najeriya

An samu karuwar hauhawar farashi a Najeriya

Farashin kayayyaki a Nigeria ya ƙaru zuwa 15.38 cikin dari, daga kashi 15.06 cikin dari da aka samu a watan Fabrairu na 2026. Wannan kuma shi ne karin farko cikin shekara guda.

Farashin kayayyaki a Nigeria ya ƙaru zuwa 15.38 cikin dari, daga kashi 15.06 cikin dari da aka samu a watan Fabrairu na 2026. Wannan kuma shi ne karin farko cikin shekara guda.

A cewar National Bureau of Statistics NBS, an samu karin 0.32% a watan Maris idan aka kwatanta da watan Fabrairu.

A ma’aunin wata zuwa wata, hauhawar farashi a watan Maris ta kai 4.18%, wanda ya fi na watan Fabrairu da 2.17%.

Wannan na nufin cewa a watan Maris na 2026, farashin kayayyaki ya ƙaru da sauri fiye da yadda ya ƙaru a watan da ya gabata.

Dangane da farashin abinci, ya kai kashi 14.31% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, yayin da a watan Maris na 2025 ya kai kashi 25.22%.

Sai dai a ma’aunin wata zuwa wata, hauhawar farashin abinci a watan Maris ta ragu zuwa kashi 4.17% daga 4.69% na watan Fabrairu.

An danganta wannan canjin da hauhawar farashin kayayyaki kamar doya, citta, rogo, gyada, dankalin turawa, ogbono, tumatir, da garin rogo.

Haka kuma, matsakaicin hauhawar farashin abinci na shekara guda zuwa watan Maris na 2026 ya kai 18.21%, wanda ya ragu idan aka kwatanta da 36.02% da aka samu a shekarar 2025.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments