Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeTinubu na tattaunawa da ƙasashen duniya ciki har da Amurka domin ƙarfafa...

Tinubu na tattaunawa da ƙasashen duniya ciki har da Amurka domin ƙarfafa tsaron ƙasa

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na neman haɗin gwiwa da Amurka da wasu ƙasashe kan batun tsaro a Najeriya.

Jakadan Najeriya a majalisar dinkin duniya, Jimoh Ibrahim, ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na tattaunawa da kasashe kan matsalar tsaro.

Ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a New York yayin da ya isa domin fara aikinsa a matsayin sabon jakadan Najeriya, inda ya tabbatar da cewa Tinubu zai magance matsalolin tsaron kasar.

Jimoh Ibrahim ya ce Najeriya ba ta takaita kan wata kasa guda ba, yana mai cewa duk wata kasa da ke da mafita ga matsalolin tsaron Najeriya ana tuntubar ta.

Ya jaddada cewa kowace kasa a duniya ta taba fuskantar kalubale a wani lokaci, inda ya kawo misali da harin ta’addanci na ranar 11 ga Satumba a Amurka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments